Kungiyar IS ta fitar da sabon bidiyo

Daya daga cikin maharan birnin Paris Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Daya daga cikin maharan birnin Paris

Kungiyar IS ta fitar da wani bidiyo da ke nuna wasu 'ya'yanta tara da suka kaddamar da hare-hare a birnin Paris a watan Nuwambar bara.

Bidiyon ya nuna wasu daga cikin mutanen suna fille kawunan wasu da kungiyar ta kama a matsayin fursinoni, sannan kuma suke atisaye irin na sojoji a yankin Gabas ta Tsakiya kafin hare haren na Paris.

Bidiyon da kungiyar ta IS ta yi wa taken "ku kashe su, duk inda kuka same su", ya kare ne da nuna lokacin da majalisar dokokin Burtaniya ta kada kuri'ar amince wa kasar ta shiga cikin masu lugudan wuta ta sama kan mayakan kungiyar a Syria.

Tara daga cikin maharan na Paris sun mutu ne a cikin daren da suka kaddamar da hare-haren, ko kuma a artabun daya biyo baya, yayin da sauran biyun suka tsere, kuma har yanzu ba a kama su ba.