Adidas zai raba-gari da hukumar IAAF

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Adidas ya ce hukumar wasannin ta dade tana rufa-rufa a kan amfani da kwayoyin kara kuzari.

BBC ta gano cewa kamfanin Adidas mai yin kayan sa wa na wasanni, yana shirin kawo karshen yarjejeniyarsa ta miliyoyin dala da hukumar shirya wasannin tsalle-tsalle da guje-guje, IAAF saboda badakalar amfani da kwayoyi masu kara kuzari da aka bankado a wasannin.

A shekarar 2019 ne ya kamata yarjejeniyar da kamfanin ya kulla da hukumar ta shekara 11 za ta kare.

Amma BBC ta gano cewa kamfanin ya yanke shawarar kawo karshen yarjejeniyar, shekara uku kafin ta kare saboda badakalar amfani kwayoyin kara kuzari da wasu 'yan wasan suka yi.

Matakin da kamfanin ya ke shirin dauka, ya biyo bayan wani rahoto da ke nuna yadda hukumar kula da wasannin tsalle-tsallen ta yi rufa-rufa game da zargin da ake yi wa Rasha na daure wa 'yan wasan kasarta gindin amfani da kwayoyin kara kuzari.

Sai dai kawo yanzu, kamfanin da hukumar kula da wasannin tsalle tsallen bas u ce komai ba game da wannan lamari.