Maleriya: Gates da Biritaniya sun hada hannu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sauro ne ke yada cutar Maleriya

Gwamnatin Biritaniya da kuma attajirin nan mai aikin jin-kai, Bill Gates, sun sanar da wani shiri na kashe dala biliyan hudu domin kawar da cutar zazzabin cizon sauro ta maleriya a duniya.

Shirin zai mayar da hankali ne wajen samar da sababbin magungunan kashe cutar, da na kashe kwari domin yaki da cutar ta maleriya.

A wani bayani da suka wallafa a wata jarida, Bill Gates da Sakataren Baitil-malin Biritaniya, George Osborne, sun ce suna da yakinin za a iya kawar da cutar maleriya baki daya a zamanin rayuwarsu.

Sun ce cutar tana kashe yaro guda a cikin ko wanne minti daya, musamman a nahiyar Afirka, kuma za a iya cewa yayin da talauci ke kawo cutar a wasu lokuta, ita ma cutar tana taimakawa wajen yaduwar talaucin.