'Kokarin kaucewa haihuwar Gilu a Brazil'

Hakkin mallakar hoto Mariana Chama

Mariana Botelho ba ta taba zaton daukar juna biyu a karo na farko zai kunshi daukar wasu matakai saboda shiga wuraren da cutar ta shafa.

Likitar, 'yar kasar Brazil mai shekaru 33, ta ce ko a wani yanayi ake, ta na saka dogon wando da rigar mai dogon hannu a ko da yaushe. Kuma ba ta saka silifa, sai dai sau ciki kawai.

Amma kuma a watanni uku da suka wuce, Mariana tana daukar matakai domin kare kanta daga cizon Aedes aegyptu, sauron da ke janyo cutar Zika.

"Idan na je wuraren da hadarin kamuwa da cutar ya fi yawa, kamar wuraren shakatawa masu lambuna dayawa, ina amfani maganin kwari," in ji Botelho.

"Kuma ni da mijina muna rufe kofar gida tun daga karfe biyar na yamma, saboda a lokacin ne saurayen suka fi yawa.Kuma yanzu ya zama kwarare a wajen kisan sauro."

A lokacin da da Mariana ta samu juna biyu, Kasar Brazil ba ta da masaniya a kan cewar kwayar cutar, wadda a lokacin ake ganin cewar zai iya janyo zazzabin Dengue wanda ke iya hana kwakwalwar yara ginuwa.

"Da a yau ne, ina ga da na jinkirta daukar juna biyu", in ji ta.

An kiyasta cewar, duk shekara, ana haifar a kalla jarirai 150 a kasar Brazil da cutar da ke hana kwakwalwar jarirai ginuwa wato microcephaly, wadda za ta iya zama sanadiyar rashin daidaiton kwayoyin halittar dan adam ko shan magunguna ko kuma wasu cututtukan da yara ke kamuwa da sui kamar 'rubella da syphilis'.

Ma'aikatar lafiya ta kasar Brazil ta ce, daga Oktobar shekarar 2015 har zuwa mako na biyu na watan Janairun wannan shekarar, kasar ta samu rahotanni 3, 893 na jariran da ake haifa da tawaya wato jariri mai karamin kai.

Hakkin mallakar hoto Mariana Chama

An fara gano yawaitar karuwar cutar ce a arewa maso gabashin Brazil kuma daga baya sai aka gano tana da dangantaka da kwayar cutar Zika a lokacin da mace ta ke da ciki, wadda aka alakanta da haddasa haihuwar gilu.

Cutar na yaduwa ne ta hanyar sauron da ke yada cutar zazzabin Dengue da kuma Chikungunya, wacce kasar Brazil ta kasa shawo kanta a cikin shekara 10 da ta wuce.

"Zan so shi kamar kowa"

Hakkin mallakar hoto AFP

A lokacin da likita ya sanarwa Valeria Barros mai shekaru 17 cewar akwai yiwuwar jaririnta yana da cutar microcephaly, nan ta ke sai ta ji kamar ta yi kuka.

An haifi jaririn da dan karamin kai, wanda da kadan girman kan nasa ya wuce na masu cutar, amma an gano ya kamu da cutar ce saboda Valeria ta nuna alamun cutar Zika a farkon lokacin da ta ke da ciki.

A halin da ake ciki, hanya daya ce kawai ake bi wajen gano kwayar cutar a jikin maralafiya, ana gano ta ne kawai idan ta kankama a jikin mutum.

Masana kimiya na fuskantar kalubale wajen ganowa ko mace mai juna biyu ta kamu da kwayar cutar a watanni da suka wuce a lokacin da suke kokarin dangatakar da ke tsakanin kwayar cutar and tawaya.

Zai iya daukan watanni kafin a tabbatar da halin da jariran irinsu Valeria da sauran matan da su ke rayuwarsu a yankuna karkara su ke ciki.

A wannan lokacin, ana yi wa da su da jariran su gwaje-gwaje daban-daban domin a gano ko kwakwalwar jaririn ta tabu kuma me ya jawo hakan.

'Buri'

Hakkin mallakar hoto Flavio Former

Iyaye wadanda suke jiran sakamakon gwajin da aka yi wa jariransu da ma wadanda aka tabbatar musu abin da sakamakon gwajin ya nuna, suna fargabar abin da ka iya biyo bayan a gano jariransu suna fama da tawaya (gilu ne).

Likitoci ba su iya fadin takamemen abin da zai iya faruwa da yaro, tun da cutar ta na taba sassa daban-daban na kwakwalwar ta hanyoyi da dama.

"Buri na shi ne ya iya zuwa jami'a. Likita ya ce ba zai iya zuwa jami'a ba, amma da Allah na dogara", a cewar Rika Roque mai shekaru 20.

Mata kamarsu Erika suna tausar zuciyar juna ta hanyar bai wa junansu labarinsu da kuma suna baiwa juna shawawari kan riga-kafin kamuwa da cutar a kafafen sada zumunta kamar WhatsApp.

Wani shafin Facebook, wanda ake amfani da shi domin yaki da cutar microcephaly, ya samu masu kaunarsa kusa 1,500 tun da aka samar da shafin a karshen watan Nuwamba.