Fulani sun yi zargin sanya musu guba a abinci

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Fulani makiyaya a Najeriya

A Nigeria, wasu Fulani mazauna kauyen Tede da ke jihar Oyo a kudu maso yammacin kasar sun koka da abin da suka kira barazanar da suke fuskanta a rayuwarsu.

Fulanin sun ce a yanzu haka akwai 'yan uwansu sama da 15 da suke zargi makwabtansu sun zuba musu guba a abinci, abin da ya kai ga mutuwar su.

Fulanin sun ce saboda fargaba, yanzu ba sa iya sayen abinci ko ruwan sha idan ba sun samu tabbacin lafiyar abincin ba.

Sun shaida wa BBC cewa suna zargin makwabtansu da hada baki da wasu jami'an kiwon lafiya a asibitin da ke yankin da hada baki domin ba su gurbatattun magunguna.

Fulanin sun yi zargin cewa ana bai wa yaransu kwayoyin da suka daina aiki a asibitin idan ba su da lafiya, lamarin da yakan zama matsala ga yaran, har ya kai ga mutuwarsu.

Kazalika, Fulanin sun ce makwabtan nasu suna sanya guba wuraren da dabbobin Fulanin ke kiwo, abin da shi ma yake kashe dabbobin nasu.

Sun kuma yi zargin cewa ana karbar kudi a hannunsu a kan cewa za a shawo kan matsalar, amma har yanzu shiru.

Sai dai rundunar 'yan sandan jihar Oyo ta musanta zargin da Fulanin ke yi, ko da ya ke ta ce tana da masaniya game da korafin sanya wa dabbobin Fulanin guba a abinci.

Rikici tsakanin Fulani da manoma Yarbawa tana kara daukar sabon salo, inda Fulanin ke cewa yanzu abin ya tashi daga kan dabbobinsu, ya koma kansu.