An kashe mutane 20 a Adamawa

Hukumomin tsaro a Najeriya sun ce 'yan bindiga sun kashe mutane 20, cikinsu har da wani babban jami'in 'yan sanda a jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin kasar.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Othman Abubakar, ya shaida wa BBC cewa wasu maharan da ake zargi makiyaya ne suka kai harin a karamar hukumar Girei da ke jihar, lamarin da kuma yi jikkata mutane da dama.

Wasu rahotanni sun ce yawan mutanen da abin ya shafa sun fi haka, inda wasu suka ce yawan mutanen da suka rasa rayukansu ya haura 30.

Rahotanni dai na cewa al'amura sun daidaita a yanki.

Ana zargin makiyayan ne da kai harin ramuwar gayya ne kan manoma, kuma an yi wa 'yan sandan kwanton-bauna ne a lokacin da yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa garin domin shawo kan rikicin.