An kara farashin kalanzir a Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gidajen man NNPC ne za su sayar a kan sabon farashin

Hukumar kula da kayyade farashin albarkatun man fetur a Najeriya, PPPRA ta sanar da kari a farashin kalanzir a kasar daga Naira 50 zuwa Naira 83 kowacce lita.

Sanarwar da hukumar PPPRA ta fitar, ta ce gidajen mai na gwamnati mallakar NNPC ne kawai za su dinga sayar da kalanzir din a wannan sabon farashin.

Hakan na cikin matakan da gwamnati ta dauka na janye tallafin da ta ke bayarwa a kalanzir da ma wasu albarkatun man fetur a Najeriya.

Sanarwar ta nuna cewa gwamnatin kasar za ta dinga samun ribar fiye da Naira 10 a kan kowacce litar kalanzir a wannan sabon farashin.

Bayanai sun nuna cewar wannan sabon farashin ba zai yi matukar tasiri ba a kan talakawan kasar wadanda galibinsu ke sayen kalanzir din a kan fiye Naira 100 kowacce lita a hannun 'yan kasuwa.