An kwakwale idanun wani yaro a Zariya

Hakkin mallakar hoto BBC Nurah Ringim
Image caption Yaron na kwance a asibiti

Wani yaro dan shekarau hudu a karamar hukumar Zariya ta jihar Kaduna ya fada hannun wasu wadanda ake kyautata zaton masu ayyukan tsafi da sassan jikin bil adama ne.

Abin da ya jefa yaron cikin tsaka mai wuya, saboda matsafan sun kwakwale masa idanunsa biyu.

Iyayen yaron sun ce ya ci karo da wasu wadanda ake kyautata zaton matsafa ne wadanda suka kai shi wani kango, da karfi kuma suka kwakwale masa idanuwa guda biyu.

Yaron ya fada hannun matsafan ne a yayin da ya fita daga gidan su a Unguwar Ban Zazzau a Zariya don zuwa gidan makwabta.

A yanzu dai yaron yana kwance rai a hannun Allah a wani Asibiti a Zariya, ba tare da idanuwan sa guda biyu ba.

Ana zargin masu neman sassan jama'a don tsafi ko 'yan aiken su da tafka irin wannan ta'asa.