Cutar Zika za ta iya bazuwa — WHO

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Cutar ta barke ne a Brazil

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce tana sanya ran cutar Zika - wadda aka alakanta da haddasa haihuwar gilu, wato jariri mai karamin kai, za ta iya bazuwa zuwa wasu kasashe Latin Amurka da Arewacin Amurka, in banda a Kanada da Chile.

Annobar cutar wadda sauro ke bazawa, ta bazu cikin sauri a Brazil tun watan Mayun shekarar da ta shige.

Sauron Aedis ne ke haddasa cutar, sai dai masana sun ce akwai yiwuwar ta iya bazuwa ta wasu hanyoyin.

Kawo yanzu ba a gane abin da ya jawo barkewar cutar a Brazil ba.

An bai wa mata masu juna biyu shawara da su guji zuwa kasashen da ake da cutar.