Shugaba Buhari ya isa kasar Kenya

Hakkin mallakar hoto NTV
Image caption Buhari da Kenyatta a Kenya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa garin Eldoret na kasar Kenya a wata ziyara ta kwanaki uku da ya soma a kasar.

Shugaba Uhuru Kenyatta ke ya tarbi Buhari a filin jirgin sama.

Buhari tare da shugaban Somalia Hassan Sheikh Mohamoud, da kuma mai masaukin baki Shugaba Uhuru Kenyatta suna halartar halarci taron girmamawa da aka shirya kan sojojin Kenya da aka kashe a Somalia.

A yayin ziyarar shugaba Buharin zai kuma gana da Shugaba Kenyatta a kebe, kafin wata tattaunawa kan huldar cinikayya da aikin gona da yawon bude ido tsakanin jami'an gwamnatin kasashen biyu.

Kazalika, ana kuma sa ran shugaba Muhamadu Buharin zai wuce kasar Habasha domin halartar taron shugabannin kungiyar tarayyar Afrika, wato A.U.