'Denmark na sanyaya gwiwar 'yan gudun hijira'

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Dubban 'yan gudun hijira na kokarin kwarara zuwa Turai

Majalisar dokokin kasar Denmark ta amince da wasu shirye-shirye da ake ta cece kuce a kai wadanda za su kashewa masu neman mafaka gwiwar shiga kasar.

Bayan wata muhawara da aka tafka wadda wasu lokaci ta yi zafi, an amince da shirye-shiryen tare da rinjaye kai tsaye.

A karkashin dokar, za a kyale masu neman mafaka su rike dukiyar da ba wuce dala dubu da dari biyar ba -- domin kuwa za a kwace duk wani abu da ya haura haka, ko da yake banda wasu kayayyaki masu muhimmanci, kamar zoben aure.

Mattias Tesfaye dan majalisar dokoki ne a kasar ta Denmark, ya ce "babu wata dokar kare hakkin bil-adama da muke tauyewa. Duk wata doka da muka amince da ita, tana karkashin yarjejeniyar da muka sanya wa hannu."