Dakarun Kenya sun janye daga Somalia

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Rundunar sojin Kenya sun ce ficewa daga sansani wani abu ne da sojoji suka saba na sauyin waje

Dakarun sojin Kenya sun fice daga sansanin el-Ade da ke kudancin Somaliya, wanda mayakan Al-Shabaab suka kai wa hari ranar 15 ga watan Janairu.

Mai magana da yawun sojin Kenya Kanal David Obonyo, ya shaida wa BBC cewa hakan wani bangare na sauyin wajen zama da sojojin suka gaji yi.

Har yanzu dai ba a san yawan wadanda suka mutu a harin ba, sai dai rahotanni na cewa an kashe sojojin Kenya fiye da 100.

Sojoji sun ce karfin bama-baman da mayakan suka yi amfani da su sun kai wanda aka dasa a ofishin jakadancin Amurka a Nairobi a shekarar 1998, wanda ya kashe fiye da mutane 200.