Mawakin Nijar Gawo Filinge ya rasu

Image caption Gawo Filinge dan asalin Jamhuriyar Nijar ne

Allah ya yi wa shahararren mawakin nan Alhaji Mahammadu Isa, wanda aka fi sani da Mahamadu Gawo Filinge rasuwa.

Ya rasu ne a ranar Lahadin da ta gabata a garinsa na haihuwa Gawo, da ke cikin gundumar Filinge a jihar Tilabery ta Jamhuriyar Nijar.

Gawo Filinge ya rasu yana da shekara 76 da haihuwa.

Daya daga cikin fitattun wakokin marigayin ita ce Najeriya da Nijar daidai suke.