Matsalar rashin aiki ta yi kamari a Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dumbin matasa ke kammala jami'a a kowacce shekara.

Wani bincike da wani kamfani mai tallata guraben ayyukan yi a Najeriya ya yi ya gano cewa akwai rashin aikin yi a tsakanin dumbin wadanda suka kammala karatun jami'a a kasar.

Kamfanin mai suna Jobberman.com, wanda yake birnin Lagos, ya ce kashi 45 cikin 100 na kusan mutane 90,000 da suka kada kuri'a a binciken nasa, ya nuna cewa ba su da aikin yi.

Kamfanin ya ce, "A bayyane yake cewa akwai bukatar kara zage dantse wajen ganin an samarwa mutane aikin yi."

A halin yanzu dai tattalin arzikin Najeiya na fuskantar matsaloli sakamakon faduwar farashin man fetur da kuma faduwar darajar kudin kasar.