An wanke Planned Parenthood daga zargi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Masu rajin hana zubar da ciki a Amurka

Wasu manyan alkalai a jihar Texas ta Amurka sun wanke cibiyar nan ta kayyade iyali, Planned Parenthood, daga zargin aikata danyen aiki, bayan an zarge ta da sayar da wasu bangarori na dan tayin mutun da ake ciro wa daga mahaifa, domin ta samu riba.

Hasalima, alkalan sun tuhumi masu rajin hana zubar da ciki da suka zargi cibiyar ne, da jirkita wasu bayanan gwamnati.

Masu rajin hana zubar da cikin sun nadi bidiyon wasu daraktocin cibiyar kayyade iyalin a cikin sirri, lokacin da suke tattauna shirin su na kai wa wata cibiyar binciken lafiya wasu sassan dan tayin mutun da suka samu ta hanyar zubar wa mata ciki.

Sai dai cibiyar ta Planned Parenthood, ta ce an yanke wasu bangarori na bidiyon da aka nada saboda a jikirkita ainihin abin da ya faru a lokacin.

A watan Nuwamban bara, ma'aikata uku na cibiyar ta Planned Parenthood ne aka kashe lokacin da wasu suka bude wuta a asibitin da suke aiki a Colarado Springs.