Ta'addanci: An damke mutane 900 a Senegal

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jami'an tsaro na shirin ko ta kwana

'Yan sanda a Senegal sun ce sun damke mutane kusan dari tara a wani sameme na yaki da aikin ta'addanci a kasar.

Sun ce sun yi kamen ne a karshen makon nan a Dakar babban birnin kasar da kuma birnin Thies da ke kusa da Dakar din.

Ma'aikatan tsaron na cikin shirin ko ta kwana ne tun bayan hare-haren da aka kai a cikin wannan watan a babban birnin kasar Burkina Faso, inda aka kashe mutane talatin.

A makon jiya ne ministan harkokin wajen kasar ta Senegal, Abdoulaye Daouda Diallo, ya yi kira ga otal otal na kasar da su tsaurara matakan tsaro ko kuma gwamnati ta rufe su.