An bayar da kyauta ga matan da suka kare budurcinsu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Za a rika yin gwaji ga matan domin ganin ba su kusanci wani namiji ba.

Gwamnar yankin KwaZulu-Natal na kasar Afirka ta kudu ta kare matakin da ta dauka na bai wa matan da ba su taba saduwa da namiji ba gurbin karo karatu a kyauta a makarantun kasar.

Madam Dudu Mazibuko ta ce ta dauki matakin ne domin hana yin zinace-zinace da kuma rage yada cutar kanjamau.

Yankin dai nayan daga cikin yankuna da aka fi samun masu fama da cutar ta kanjamau.

Madam Mazibuko ta bai wa mata 'yan makaranta 16 gurbin ci gaba da karatu a kyauta, amma da sharadin cewa ba za su bari wani namiji na kusance su ba.

Kazalika, matan da aka bai wa wannan gurbi za su rika zuwa akai-akai ana gwada su domin ganin ko sun kusanci namiji ko kuwa ba su yi ba.

Kungiyoyin kare hakkin mata sun soki wannan mataki, suna masu cewa hakan wani yunkuri ne na take hakkin dan adam.