UNICEF zai samar da tallafin karatu ga yara

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dubban yara ne rikicin Syria ya yi sanadin raba su da karatu.

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya kaddamar da wani tallafi na samar da dala biliyan biyu da miliyan 800 domin taimakawa yara a yankunan da ake fama da rikice-rikice.

Tallafin zai mayar da hankali ne a kan samar da ilimi.

UNICEF ya ce yaro daya cikin goma ne kacal ke zuwa makaranta a yankunan da ake fama da rikice-rikicen, amma hukumar tana son a rubanya wannan yawan.

Asusun na UNICEF ya kuma ce yana fatan ya taimakawa yara fiye da miliyan takwas a wannan fanni, da suka hada da wadanda suka fito daga Syria, wadanda a yanzu haka suke cikin kasar da kuma wadanda suke gudun hijira a wasu wuraren.