Birtaniya za ta dauki 'yan gudun hijira

Yara 'yan gudun hijirar Syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mata da kananan Yara na daga cikin wadanda suka fi shan wuta a rikicin Syria.

Gwamnatin Birtaniya ta ce za ta karbi karin yaran da ba sa tare da iyayensu a sansanonin 'yan gudun-hijira da ke makwabtaka da kasar Syria.

Wadannan kananan yara za su kasance kari ne ga adadin masu gudun-hijira dubu ashirin daga kasar Syria, wadanda Birtaniyar ta amince za ta karba a cikin shekara biyar masu zuwa.

Tuni dai Ministan shige-da-ficen Birtaniya, James Brokenshire ya bukaci Majalisar dinkin duniya ta rarrabe yaran da ba sa tare da iyayensu a sansanonin 'yan gudun-hijirar, kana ta taimaka wajen kai su Birtaniya.

Sai dai gwamnatin Birtaniyar ba ta fadin yawan yaran da za ta karba ba.

Amma jam'iyyar adawa ta Labour na so Birtaniyar ta karbi yara dubu uku.