An bullo da wata hanyar tsaro a Kamaru

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An haramta saka nikabi a lardin arewa mai nisa a Kamaru

Hukumomi a lardin arewa mai nisa a Kamaru sun bullo da wata sabuwar hanyar tabbatar da tsaro a tsakanin jama'a.

A yanzu haka a mabiya addinan musulunci da kuma na kirista ne suke tabbatar da tsaro na karba-karba a gaban masalatai ranar Jumma'a da kuma majami'u a ranar Lahadi.

Wannan sabon salo ne domin shawo kan yawaitar hare-hare a yakin.

Gwamnan lardin arewa Midjinyawa Bakary, ya ce matakin na gwaji ne a wasu garuruwan kan iyaka, kafin ya zama na gama gari a fadin lardin wanda shi ne yake fama da ta'addancin kungiyar Boko Haram.

Bayanai sun ce yan kungiyar Boko Haram sun kashe kimanin mutane 1,200 a Kamaru tun daga shekarar ta 2013.