Mutane 10 sun halaka a harin Chibok

Akalla mutane 10 sun rasu a yayin da wasu sama da 30 suka jikkata sakamakon hare-haren kunar bakin wake da aka kai a wurare uku a garin Chibok na jihar Borno.

Ana zargin 'yan Boko Haram da kaddamar da wadannan hare-haren.

Bayanai sun ce an tayar da bam guda a kasuwar garin da kuma daya a wurin binciken ababen hawa.

"Akalla mutane 10 sun rasu, a yayin da fiye da 30 suka samu raunuka," in ji Ayuba Chibok.

A garin na Chibok ne a 2014 aka sace 'yan mata dalibai su sama da dari biyu, wadanda har yanzu ba aji duriyar galibinsu ba.

Ahmad Abba Abdullahi ya tuntubi Malam Ayuba wani dan garin na Chibok, wanda ya ce duk da ba ya cikin garin a yanzu, amma yana da bayani kan abin da ya faru:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti