Gbagbo ya bayyana gaban kotun ICC

Laurent Gbagbo Hakkin mallakar hoto
Image caption Mutane dubu uku ne suka rasu a rikicin bayan zabe.

Tsohon shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo, ya musanta zarge zargen da ake masa a kotun ICC.

A ranar Alhamis ne Laurent Gbagbo ya gurfana a gaban kotun ta hukunta masu aikata manyan laifuka ta duniya da ke zamanta a Hague.

Mista Gbagbo shi ne tsohon shugaban kasa na farko ya bayyana a gaban kotun, inda ake zarginsa da laifukan yaki da cin razafin bil'adama a lokacin da ya ki amincewa da shan kaye a zaben shekarar 2010, wanda shugaba Alassane Ouattara ya lashe.

Mutane dubu uku ne suka mutu a lokacin rikicin bayan zaben.

Ana tuhumar Mista Gbagbo tare da tsohon shugaban mayakan sa-kai Charle Be Goude.

Magoya bayansa na ganin cewa duk da aika-aikar da dukkan bangarorin biyu suka yi a wancan lokaci, magoya bayan Mista Gbagbo kadai ake tuhuma.