Ni ne halataccen shugaban PDP — Gulak

Ahmad Gulak Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jam'iyyar PDP ta dade ta na fuskantar matsala kan batun shugabanci.

A Nigeria, rikicin shugabancin babbar jam'iyyar adawa ta PDP na kara kamari, bayan da tsohon mai ba wa shugaba Jonathan shawara kan harkokin siyasa, Barista Ahmed Ali Gulak ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban jami'iyyar na kasa.

Barista Gulak ya isa hedikwatar PDP ne a Abuja zagaye da wasu fitattun 'yan jam'iyyar da ke mara masa baya da suka hada da tsohon mai taimaka wa shugaba Jonathan a kan harkokin yada labarai Dr. Doyin Okupe.

Sai dai wasu jami'an jam'iyyar sun yi fatali da wannan matakin.

Jam'iyyar dai ta kasance ba ta da tsayyayen shugaba tun bayan murabus din da Alhaji Ahmed Adamu Mu'azu ya yi a watan Mayun bara.