Zan yi magana a nan gaba — Jonathan

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dasuki na hannun EFCC a kan batun kudin sayen makamai

A karon farko, tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce zai yi tsokaci game da dala biliyan biyu da miliyan dari daya da ya ware domin sayen makaman yakin da kungiyar Boko Haram, amma ake zargin wasu jami'an gwamnatinsa sun sace.

Mista Jonathan ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, zai yi bayani a lokacin da ya dace dangane da batun.

Ya kara da cewa ba zai so ya tsoma baki a tsarin shari'ar Najeriya ba, ganin cewa an riga an gurfanar da mutanen da ake zargi da sace kudin a gaban kotu.

Batun sace kudin sayen makaman dai ya ja hankulan 'yan kasar, musamman bayan an kama Kanar Sambo Dasuki, tsohon mai bai wa Goodluck Jonathan shawara a kan tsaro, bisa zarginsa da hannu wajen sace kudaden.

Baya ga Sambo Dasuki, an kama wasu manyan 'yan jam'iyyar PDP ta tsohon shugaba Jonathan wadanda ake zargi da raba wani bangare na kudin, cikinsu har da tsohon shugaban jam'iyyar Bello Haliru Mohammed, kakakin jam'iyyar, Olisa Metuh, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa da mai gidan talabijin na AIT, Cif Raymond Dokpesi.