An rantsar da gwamna a Kogi ba mataimaki

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello Hakkin mallakar hoto Bello
Image caption Faleke da APC sun shiga yanayin sa-toka sa-katsi ne tun bayan mutuwar Yarima Audu a watan Nuwamban bara

A Najeriya, an rantsar da Yahaya Bello a matsayin sabon gwamnan jihar Kogi, ba tare da mataimakinsa James Faleke ba.

Babban jojin jihar Nasir Ajana ne ya rantsar da sabon gwamnan a ranar Laraba.

Sai dai Shugaban kwamitin yada labarai na kwamitin da jam'iyyar APC ta kafa na shirya rantarwar Isiaq Ajibola, ya tabbatar wa da BBC cewa Faleke bai halarci wajen rantsarwar ba.

Faleke ya kauracewa rantsarwar ne saboda matakin da jam'iyyarsa ta dauka na kin neman kotun sauraron kararrakin zabe ta tabbatar da shi a matsayin sabon gwamna, bayan mutuwar yarima Abubakar Audu.

Wannan ne dai karo na farko da aka taba rantsar da gwamna ba tare da mataimaki ba a tarihin siyasar Najeriyar.