Amurka na son yin kasuwanci da Nigeria

Hakkin mallakar hoto mark knoller
Image caption Amurka ta nuna sha'awar son yin mu'amala da Najeriya a harkoki daban-daban.

Wata tawagar 'yan kasuwar Amurka ta ziyarci shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, a fadarsa da ke Abuja.

Sakatariyar Cinikayya ta Amurka Ms Penny Pritzker, wadda ta jagoranci tawagar ta shaida wa shugaban kasar cewa sun zo Najeriya ne domin su fahimci irin dama da kuma kalubalen da ake cin karo da su ta fuskar kasuwanci a kasar.

Ta ce shugaban Amurka Barack Obama ne ya turo su domin duba hanyoyin da za su kara yin aiki tare da gwamnatin Najeriya.

Baya ga harkar kasuwanci, a baya ma dai Amurka ta so taimakawa Najeriya ta fuskar tsaro da sauran al'amura.