Kasuwar manyan wayoyin Samsung ta fadi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Samsung

Kamfanin Samsung ya gamu da koma-baya wajen sayar da manyan wayoyinsa da sauran na'urorin da ke alaka da su.

Ana dai danganta faduwar kasuwar ne da raguwar bukatar kayan kamfani a kasuwa, inda ribar kamfanin ta ragu da kashi 40 bisa dari a karshen watan Disamban da ya wuce, wato dala biliyon biyu da miliyon dari bakwai.

Kamfanin Samsung din dai tuni ya bayyana fargabar cewa da wuya bana ya ci irin ribar da ya samu a bara.

Kamfanin dai ya yi kukan cewa babbar wayarsa samfurin Galaxy S6, wadda aka kaddamar a watan Afrilun ta gaza jan hankalin masaya, lamarin da ya tilasta wa kamfanin shiga kokawar daidaita hannayen-jarinsa a kasuwa.

Sai dai Kamfanin ya bayyana cewa zai ci gaba da kera wasu sababbin wayoyi, duk kuwa da irin kalubalen da yake fuskanta.