Zanga-zanga kan dokar zubar da ciki a Saliyo

Hakkin mallakar hoto ap
Image caption Shugaba Bai Koroma ya ki sanya hannu kan dokar.

Shugabannin Kirista da Musulmai a Saliyo sun yi kira ga al'ummar kasar wajen hada kai domin yin tattaki zuwa majalisar dokoki don neman a janye wata doka mai cike da rudani a kan zubar da ciki.

Ita dai wannan doka da ake son gabatarwa za ta bayar da damar a zubar da cikin da ya kai har makonni 12 ne ba tare da wata kwakkwarar hujja ba.

Wannan ne abin da ya kawo rudanin har Malaman addini ke ganin dokar ba ta kunshi komai ba illa kisan kai na ba gaira ba dalili.

Amma masu goyon bayan dokar sun ce hakan zai taimakawa wajen kawo karshen zubar da cikin da ake yi ba bisa ka'ida ba, wanda yake yawon jawo mace-macen mata.

Sai dai dokar ta ce ba za a halatta zubar da cikin da ya kai makonni 13 zuwa 24 ba sai in har lafiyar uwa na cikin barazana.

A watan Disambar da ta gabata ne majalisar dokokin ta gabatar da kudurin amma shugaban kasar ya ki sanya hannu bayan da shugabannin addinai suka kai mata korafinsu.