Me yasa China ke jan hankalin manyan 'yan kwallo?

Ko wadanne dalilai ne suka sa China ke jan hankalin manyan 'yan kwallon duniya da Kochiyoyi?

Kulob din Jiangsu Suning na kasar China na daf da sayen dan wasan kulob din Chelsea Ramires kan kudi fam miliyan 25.

Amma wanne dalili ne zai sa dan wasan mai shekaru 28 dan kasar Brazil, ya zabi barin kungiyar Chelsea ta zakarun Turai zuwa kungiyar da ta zo matsayin na tara a gasar kwallon China cikin shekarar 2015?

Dan wasan tsakiyar wanda ya koma kulob din Chelsea daga Benfica kan kudi fam miliyan 17 a shekarar 2010, ya buga wasanni bakwai ne kawai a Firimiyar Ingila a kakar wasannin bana.

Remirez na matukar shan wahalar samun damar buga kwallo tun da kocin rikon kwarya Guus Hiddink, ya karbi jagorancinsa.

Amma me yasa sai China?

Watakila akwai wata alakar da kulob din Jiangsu yake da ita da kulob dinsa na Chelsea ne ga 'yan wasa masu tasowa.

Tsohon dan wasan Chelsea, Dan Petrescu shi ne yake jagorantar kungiyar ta China.

Baya ga haka kuma, wasu daga cikin manyan 'yan wasan Brazil na duniya suna tallata kansu a China.

'Alakar Brazil'

Daga cikin fitattun 'yan wasan akwai tsohon dan wasan tsakiya na kulob din Tottenham Hotspur, Paulinho.

Ya sanya hannu kwangila a kungiyar Guangzhou Evergrande a watan Yunin 2015 kan yarjejeniyar shekara hudu kan kudi kusan fam miliyan 10.

Tsohon dan wasan wanda ya buga wa Real Madrid da Manchester City da AC Milan ya kuma buga wa kungiyar Guangzhou a kakar wasan bara.

Ya samu kansa a kungiyar da yawanci 'yan Brazil ke ciki wacce kuma dan Brazil din ne ke jagorantarta wato Luiz Felipe Scolari.

Hakkin mallakar hoto AFP
'Armashin buga wasa a wasu kasashen'

Scolari ya sake samun nasarar cin kofin duniya a karkashin kungiyar Guangzhou da Fabio Cannavaro dan kasar Italiya wanda ya maye gurbin wanda ya lashe gasar cin kofin duniya da kuma tsohon shugaban kungiyar Italiya Marcello Lippi.

Akwai kuma Sven-Goran Eriksson.

Shi ne mai jagorantar kungiyar Shanghai SIPG, ya kuma kasance a China tun shekarar 2013, har ma kuma a baya-bayan nan ya nemi dan wasan Manchester United Wayne Rooney shi ma ya koma kungiyar.

Idan ana batun yadda rayuwa take a China kuwa, dan wasan na matukar nuna jin dadin kasancewarsa a can.

Ya ce, "wannan kasa ce mai dadin zama. Ina zama ne a Shanghai, kuma idan aka ce na kwatanta garin da London, gaskiya kai tsaye ba zan iya cewa ga wadda ta fi ba."

'Masu gidan rana'

Ko da yake dai ana ganin yiwuwar komawar Rooney China abu ne da zai iya jawo muhawara, to ana ganin dai kudin da za a biya shi irin wanda da wuya mutum ya iya dauke idonsa a kai ne.

'Yan wasan Biritaniya da suka koma China dai zuwa yanzu su ne, Maurice Ross a shekarar 2010 da Derek Riordan a shekarar 2011 da kuma Akpo Sodje a shekarar 2012.

Kazalika daya daga cikin manyan 'yan wasan kungiyar ta Shanghai, shi ne dan wasan Sunderland Gyan, wanda yake farin ciki cewa ya yi gam-da-katar yana samun masu gidan rana.

Ana ganin ya kamata ya zamo daya daga cikin 'yan wasan da aka fi biyansu a watan Yulin bara.

Dan wasan dan kasar Ghana ya samu kimanin kudi fam miliyan 247,000.

Wanda a iya cewa kawai manyan 'yan wasa irin su Lionel Messi da Cristiano Ronaldo ne suka fi shi cafkar kudi.

'Ci gaba'

Da irin wannan kudi da ake samu, akwai alamun nan gaba yawan 'yan wasan da za su koma yankin Gabas mai nisa buga tamaula za su kara yawa.

Yawan 'yan wasa na karuwa, kudi ma kuma na karuwa.

Dukiya da yawan al'ummar da ke China sun sanya harkar wasanni ta zama kasuwancin da ke kawo makudan kudi , kuma a bayyane yake cewa kungiyoyin kwallo na China za su ci karensu ba babbaka, Ramires zai iya tabbatar da hakan.