An bude iyakar Sudan da Sudan ta Kudu

Omar al-Bashir Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yakin basasar Sudan da Sudan ta Kudu raba 'yan kasar da muhallansu.

Kafafen yada labaran kasar Sudan sun ce a karon farko, tun lokacin da aka ba wa Sudan ta kudu 'yancin kai, an bude iyakar da ke tsakanin kasashen biyu, wato shekaru biyar kenan da suka shude.

Matakin da shugaban Al Bashir ya dauka na bude iyakar ya biyo bayan shawarar da Sudan ta kudun ta yanke ta janye sojojinta daga kan iyakar, da kuma aniyarta ta tura jakadanta zuwa Karthoum, babban birnin Sudan a kokarin da ake yi na kyautata hulda tsakanin kasashe biyun.

Kasar Sudan dai ta rufe iyakarta da Sudan ta kudu ne a shekara ta 2011 sakamakon zargin da ta yi cewa Sudan ta kudun na tallafa wa 'yan tawayen a arewacin kasar.

Kazalika a baya, kasashe biyun sun kara da juna a kan wani yanki mai arzikin mai da ke kan iyakarsu.