Apple ya janye fulogi daga kasuwa

Hakkin mallakar hoto apple
Image caption apple plug

Kamfanin Apple ya janye wasu miliyoyin fulogai daga kasuwa saboda dalilai na kariya

Kamfanin ne ya taimaka wajen fayyace fulagan da suke da illa da nufin kare al'uma don kada wuta ta ja su, bayan an fahinci cewa wasu daga cikin fulagan suna karyewa.

Kamfani ya bayyana cewa ya samu labarin aukuwar hadari daban-daban har sau 12 daga jama'a kafin ya dauki matakin janye fulogan daga kasuwa.

Fulogan da matakin ya shafa galibi suna zuwa ne a cikin setin kumfuta samfurin Mac da na'urorin iOS da aka sayar a nahiyar Turai da kuma wasu kasashe biyar a duniya daga shekara ta 2003 zuwa 2015.

Sauran kasashen da lamarin ya shafa sun hada da Argentina da Brazil da New Zealand da Koriya ta kudu.

Kamfanin dai ya ce ofisoshinsa da ke kasashen zai yi wa jama'ar da lamarin ya shafa musanyar fulogan.