'Yan kunar bakin wake sun halaka mutane a Kamaru

Hakkin mallakar hoto .
Image caption Dakarun Kamaru sun jiran ko-ta-kwana

'Yan kunar bakin wake mata su biyu sun tayar da bam a wata makarantar Firamare da ke Kerawa, a lardin arewacin Kamaru.

Bayanai sun ce 'yar kunar bakin wake daya ta tayar da bam a cikin harabar makarantar inda ta halaka mutane biyu sannan wasu hudu kuma suka jikkata.

Wani mazaunin garin ya shaida wa BBC cewa daya 'yar kunar bakin waken ta tayar da bam din da ke jikinta a lokacin da 'yan sintiri ke kokarin hana ta kutsawa cikin makarantar.

Kafin wannan aika-aikar, tun da safe a ranar Alhamis, 'yan kungiyar sintiri ta Vigilante sun damke wasu mata biyu 'yan kunar bakin wake kafin su tafka ta'asa.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomi a lardin arewa mai nisa a Kamaru suka bullo da wata sabuwar hanyar tabbatar da tsaro a tsakanin jama'a.

Mabiya addinan musulunci da kuma na kirista ne suke tabbatar da tsaro na karba-karba a gaban masalatai ranar Jumma'a da kuma majami'u a ranar Lahadi.