An kama wani da makamai a Faransa

Image caption A karshen shekarar da ta gabata ne aka kai wani babban hari birnin Paris.

'Yan sandan Faransa sun kama wani mutum dauke da makamai a wurin wasan yara na Disneyland da ke birnin Paris.

Jami'ai sun ce mutumin na dauke da bindigogi biyu da jakar harsasai da kuma Al-qurani a akwatinsa.

An gano bindigogin ne ta na'urar tantancen abubuwa a wurin binciken kofar shiga Otal din wurin wasan yara na Disneyland.

Rahotanni sun ce ana kuma tsare da wani abokin mutumin mai shekaru 20.

Tun bayan harin da 'yan ta'adda suka kai birnin Paris a shekarar da ta gabata ne jami'an tsaro a Faransan sun karfafa tsaro a kasar.

A halin yanzu, an kafa dokar ta baci a kasar.