'Yan Nigeria masu sa mata karuwanci a Turai

'Yan Sandan Catalan na kai samame
Image caption Matsalar safarar mutane ta shafi kasashe da dama

A bara ne wakilin BBC Sam Piranty, ya samu wata dama daga dan sandan Catalan, Mossos D'Esquadra domin yin bincike kan gungun 'yan Najeriya da ke safarar mutane domin sanya su karuwanci.

Piranty ya yi magana da masu safarar mutanen da kuma matan da aka ceto daga bautar karuwanci, gabannin ya dauki hoton bidiyon wani samame da 'yan sanda suka kai a farkon watan Nuwamban shekarar da ta gabata, wanda ya kai ga cafke mutane 23.

Haka kuma ya gano cewa a yanzu gungun na amfani da London a matsayin wata hanyar shiga nahiyar Turai.

Da karfe takwas na safiya ne a agogon hedikwatar 'yan sandan Catalan da ke wajen garin Barcelona, shugaban yaki da safarar mutane Xavi Cortes na tsaye yana jiran tawagarsa ta mutane 22 domin tabbatar da cewa sun shirya. Sannan ya ba da umarnin kai samamen.

Hakan ne kuma ya kai ga kama wasu shugabannin wata kungiya ta 'yan Najeriya da ke zaune a Barcelona wanda ke safarar mutane.

Image caption An samu fasfunan bogi na Nigeria yayin samamen

Sunan kungiyar Supreme Eiye Confraternity (SEC), ko kuma the Air Lords, a turance, Inda aka cafke 23 a cikinsu.

An dai kwashe tsawon watanni 18 ana shirya kai wannan samame wanda ya kunshi sauraro da satar bayanan miliyoyin wayoyin salula da kuma sanya ido akan abin da ke gudana.

Kungiyar masu safarar mutanen ta somo asali ne a jami'ar Ibadan a shekarun 1970, kuma dalilin kafa ta tun asali shi ne taimaka wa al'umma.

Amma da tafiya ta yi tafiya sai wakilanta suka fara kaucewa hanya suna aikata manyan laifuka a Najeriya da kasashen ketare.

A yanzu kungiyar na safarar mutane ne da kuma muyagun kwayoyi kamar su hodar ibilis da tabar wiwi tare da yin fasfuna na bogi.

Haka zalika kungiyar tana da hannu wajen shigar da danyen mai na sata zuwa nahiyar Turai.

Dan sandan da ke shugabantar yaki da safarar mutane Cortes ya ce "Suna da hanyoyi da dama da suke bi na samun kudade, amma mu mun fi maida hankali ne kan safarar mutane da kuma wadanda aka yi safarar tasu."

Mataimakin Cortes wato Alex Escola ya kara da cewa "Wani bayanin da ke daga hankali wanda muka ci karo da shi ta hanyar satar sauraron maganarsu ta wayoyin salula shi ne, a ranar bakwai ga watan Yulin 2015, kimanin wakilan kungiyar ta SEC 400 ne suka yi wani taro a Geneva."

Image caption Safarar mutane na ciwa 'yan sandan Catalan tuwo a kwarya

Birnin Benin na Najeriya dai wata matattara ce ta safarar mutane kuma wuri ne da ya dace da a sanya ido domin ganin yadda suke ayyukansu.

Bayan wani dogon tattaunawa, tawagar BBC ta samu yin magana da wani mai samo mata, inda ya ce suna samun 'yan mata idan sun kawo kansu ko ta hanyar iyalansu idan sun yi musu alkawarin sama musu ayyukan bogi a manyan kantuna ko kuma shara.

Sai dai wasu na da cikakkiyar masaniyar cewa za a tura su karuwanci ne a Turai.

Destiny na da shekaru 19 a lokacin da aka yi safararta zuwa Spaniya shekaru uku da suka wuce, kuma ta shaida wa BBC cewa ta san za ta yi karuwanci, amma bata zaci za a bautar da ita ta hanyar lalatar ba.

Wata kungiya mai zaman kanta a birnin Benin ta ce a yanzu masu samo 'yan matan kan fita wajen gari ne domin neman wadanda basu da labarin gaskiyar abin da ke faruwa.

Kuma da zarar sun samu mata sai a kai su Legas ko arewacin Najeriya, kana a mika su ga wadanda zasu yi jigilarsu.

Image caption Wasu cikin wadanda ake safarar na mutuwa a cikin sahara

Tafiya zuwa Turai na cike da haddura domin matan da masu jigilarsu kan gamu da kungiyoyin masu dauke da makamai a cikin Sahara a Nijar ko kuma a Libya, inda ake bukatar su biya dubban kudaden euro kafin a barsu su wuce.

Daga nan ne kuma za a kai matan ga wasu mutane a Libya kafin a tsallakar da su zuwa nahiyar Turai, sai dai mazan da ke gadinsu na yi musu fyade har ma ta kai ga wa matan su dauki ciki. Yayin da kuma ake gana wa wadanda suka ki yarda su yi karuwanci azaba.

Kwanaki kadan bayan kai samamen da 'yan sanda suka kai Barcelona ne dai Cortes ya nuna rashin gamsuwarsa, yana mai cewa al'amarin babba ne domin da zarar sun cafke masu safarar kungiyar zata maye gurbinsu saboda girmanta da rassa da take da su a duniya, abin da yasa yake ganin yaki ne da ke bukatar sa hannun 'yan sanda na duniya.