Ku lalubo hanyoyin samun kudi — Udoma

Hakkin mallakar hoto
Image caption Buhari a lokacin da yake gabatar da kasafin kudi a majalisa

Ministan kasafin kudi da tattalin arziki na Najeriya ya yi gargadin cewa ci gaba da faduwar farashin mai a duniya zai yi mummanan tasiri ga tattalin arzikin kasar.

Sanata Udoma Udo Udoma ya ce akwai yiwuwar faduwar da farashin danyen man yayi zai dore, kuma hakan zai shafi yawan kudaden shigar da gwamnatin tarayya kasar ke samu tana rabawa ga sauran matakan gwamnati na jihohi da kananan hukumomi.

A cewarsa, saboda haka dole jihohin kasar su kara lalubo wasu hanyoyin da za su samar wa kansu kudade a maimakon dogara kacokan kan kason gwamnatin tarayya.

A yanzu haka saboda faduwar farashin mai a kasuwar duniya, Najeriya ta bullo da wasu hanyoyi musamman na takaita musayar kudaden waje a matsayin daya daga cikin hanyoyin rage rashin tabbas da tattalin arzikin ya shiga.

Shugaba Muhammadu Buhari ya sha nanata cewar ba zai rage darajar kudin kasar ba watau Naira a matakin rage matsalar da tattalin arzikin ya shiga.