Farashin mai ya dan samu tagomashi

Image caption Farashin mai ya yi watanni yana tanga-tangal

Farashin Gangan mai ya hau da fiye da kashi 6 cikin 100 inda ya zama dala 35 ko wacce ganga daya, irin tashin da bai yi ba a cikin watanni uku.

Wannan ya zo ne bayan ganawar da Rasha ta yi da Saudiyya a kan rage yawan fitar da man.

Rasha ta ce gwamnatin Saudiyya ta bukaci ko wacce kasa mai samar da danyan mai su rage kashi 5 cikin dari domin a tallafawa faduwar farashin man.

Sai dai har yanzu ba a cimma wata yarjejeniya ba tukuna.

A farkon wannan watan ne, farashin mai yayi faduwar da bai taba yi ba a cikin shekara guda, abin da ya janyo rashin tabbas a kasuwar hannayen jari a duniya.