An kai hari a wani masallacin Saudiyya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Harin ya shafi mutane da dama.

Jami'ai a kasar Saudiyya sun ce akalla mutane uku ne suka mutu a harin da wasu 'yan bindiga suka kai a wani masallacin 'yan Shia lokacin suna yin sallar Juma'a.

Sun kara da cewa mutane da dama sun jikkata a harin, wanda aka kai a masallacin Imam Reza da ke garin Mehasin na gabashin kasar.

Wani ganau ya ce masallata sun tsayar da daya daga cikin maharan, wanda ya yi yunkurein tayar da bam din da ke jikinsa.

Jami'an tsaro sun yi gaggawar yi wa masallacin kawanya.

Sau da dama dai 'yan kungiyar IS da ke ikirarin kishin Musulinci sun kai wa 'yan Shi'a hari.

Harin na yau ya faru ne a lokacin da ake yin zaman tsama tsakanin Saudiyya da Iran bayan Saudiyyar ta kashe wani fitaccen dan Shi'a a watan Disamba.