WHO ta kira taron gaggawa kan Zika

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Cutar Zika ke janyo haihuwar Gilu

Hukumar Lafiya ta duniya, WHO ta kira taron gaggawa a Geneva a ranar Litinin mai zuwa domin tattauna abin da ta kira habakar yaduwar kwayar cutar Zika wanda aka danganta da haihuwar jarirai da nakasa.

Shugabar WHO, Margaret Chan ta ce an sami rahotannin cutar wadda sauro ta haddasawa, ta bazu a kasashe 23 da kuma wasu yankuna na arewaci da kudancin Amirka.

Ta ce yadda kwayar cutar ke yaduwa yana da tayar da hankali matuka.

Bugu da kari ta ce halin yanayin da ake ciki na iya kara yaduwar sauro a yankuna da dama.