EFCC ta kama tsohon babban hafsan sojin sama

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Air Marshal Amosu mai murabus na hannun EFCC

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC, ta kama tsohon babban hafsan sojojin saman kasar, bisa zargin karkatar da kudaden siyo makamai.

Tun a ranar Laraba, EFCC ta tsare Air Marshal Adesola Amosu, domin ci gaba da yi masa tambayoyi kan rawar da ya taka a badakalar siyo makamai domin sojojin kasar su yi yaki da kungiyar Boko Haram.

Yana daga cikin manyan tsaffin jami'an tsaro 20 da shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umurnin a yi musu tambayoyi bisa zarginsu da hannu wajen aikata almundahana.

A yanzu haka Kanar Sambo Dasuki, mai bai wa tsohon shugaban kasar shawara a kan tsaro, ya gurfana gaban kotu kan zargin wawure kudin sayen makamai, amma dai ya musanta zargin.

Tuni gwamnatin Najeriya ta kafa kwamiti mai karfi domin tabbatar da cewa, duk wanda ya aikata laifin yin sama da fadi da kudin sayen makamai bai kaucewa hukunci ba, yayin gurfanar da shi a gaban shari'a.