Shi'a: El-Rufai ya rantsar da kwamiti

Image caption Kwamitin na da wakilai 13

Gwamna Nasir Ahmed El-Rufai ya rantsar da kwamitin shari'a domin binciko musabbabin rikicin da ya faru a Zaria ta jihar Kaduna tsakanin sojojin da 'yan mazhabar Shi'a.

Gwamnatin jihar Kaduna ta kafa kwamitin mai wakilai 13 ne a karkashin jagorancin wani babban alkali na kotun daukaka kara ta tarayya, Mai shari'a Mohammed Lawan Garba.

Kwamitin dai na da alhakin gano abin da ya haddasa arangamar, da adadin mutanen da suka rasu ko suka bata da kuma yadda za a kawo karshen irin wannan rikicin a gaba.

Sai dai kungiyar 'yan Shi'a ta yi watsi da kwamitin, inda ta ce wasu wakilan kwamitin ba za su yi musu adalci ba.

A cikin watan Disamba ne rikici ya barke tsakanin sojoji da 'yan Shi'a a Zariya, lamarin da ya janyo rasuwar mutane da dama.

A yanzu dai jami'an tsaro na tsare da shugaban 'yan Shi'a, Sheikh Ibrahim El-zakzaky tun bayan da aka yi tashin hankalin.