Jam'iyyun adawa sun ki sa hannu kan kundin da'a a Nijar

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hama Amadou na daga cikin 'yan takara a jam'iyyun adawa

Kawancen jam'iyyun siyasa 'yan adawa a Jamhuriyar Nijar sun kaurace wa sa hannu a kan wani kundin yin ladabi da da'a wanda sauran jam'iyyu na bangaren masu mulki da 'yan ba ruwanmu suka sa wa hannu.

'Yan adawar sun ce sun ki sa hannun ne domin nuna rashin amincewarsu da ci gaba da tsare abokansu a gidajen kaso ba bisa ka'ida ba.

Shi dai kundin yin ladabin da oda na nufin daukar matakan tafiya zabe mai zuwa cikin kwanciyar hankali.

A ranar 21 ga watan Fabrairu ne za a gudanar da manyan zabuka a jamhuriyar Nijar, inda shugaba mai ci Muhammdou Issufou tare da sauran 'yan takara irin su Hama Amadou za su fafata.