Metuh ya fito daga kurkuku

Hakkin mallakar hoto EFCC
Image caption Metuh ya biya naira miliyan 400 na beli.

An saki mai magana da yawun jam'iyyar PDP Olisa Metuh, daga kurkuku bayan da ya cika sharuddan da aka sa masa na beli.

A ranar 19 ga watan Janairu ne kotu ta bayar da belin Mista Metuh bisa sharadin biyan naira miliyan 400, da kuma gabatar da mutane biyu da za su tsaya masa.

Dokar ta ce su ma wadannan mutane biyu dole ya kasance suna da kadarori a gundumar Maitama da ke Abuja, babban birnin tarayya, kuma kowannensu sai ya biya naira miliyan 200.

An zargi Mista Metuh ne da karbar naira miliyan 400 daga tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro Sambo Dasuki cikin kudin sayen makamai da ake zargin ya karkatar da su.