An fara muhawara babu Donald Trump

Mr Trump Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Trump ya na fushi da wadanda suak shirya gasar, shi ya sa ya kaurace ma ta.

Mai neman tsayawa takarar shugabancin Amurka a karkashin jam'iyyar Republican, Donald Trump, ya ki shiga wata babbar muhawarar jam'iyyar, wadda ake yi ta talabijin.

Mista Trump dai na fushi ne da wadanda suka shirya gasar, wato gidan Talabijin na Fox News, don haka ne ma ya yi tafiyarsa wajen wata gidauniyar tallafa wa mazan-jiya, kuma ya ce yana kokarin kare hakkinsa ne, saboda bai ji dadin abin da gidan talabijin din ya yi masa ba, a wata muhawarar da aka yi a baya.

Sai dai gidan talabijin din, a nasa bangaren ya ce Mista Trump ya bukace shi da ya ba da dala miliyan hudu a matsayin gudunmowa ga gidauniyar mazan-jiyan, kafin ya halarci muhawarar.

Wannan muhawarar da ake yi a garin Iowa dai ita ce muhawarar jam'iyyar Republican ta karshe gabannin tsayar da dan takara, kuma da ita ake rarrabewa tsakanin kwai da dutse cikin masu neman tsayawa takarar.