Shugabannin Afirka na taro a Ethiopia

Shugabannin kasashen Afirka na gudanar da taron koli yau wanda suka saba yi duk shekara a Addis Ababa babban birnin Ethiopia.

A yayin taron ana sa ran za su kada kuri'a a kan wani shiri na tura sojoji 5000 na kiyaye zaman lafiya zuwa Burundi.

Ana bukatar samun kashi biyu cikin kashi uku na kuri'un da shugabannin za su kada kafin a amince da tura sojojin.

Sai dai Burundi ta na adawa da shirin tura sojojin ta na mai cewa yin hakan tamkar wani yunkuri ne na yi wa kasar mamaya.

Kungiyar tarayyar Afirkar dai na son tura sojojin ne domin kare fararen hula a Burundi.

An kashe daruruwan jama'a tun bayan da shugaba Pierre Nkurunziza yace zai tsaya takara karo na uku a karagar mulki.