An kai hari a Chadi

Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption Ana zargin Boko Harm da kai hare-haren guda biyu na yankin tafkin Chadi

Akalla mutane 3 suka mutu yayin da kuma wasu 56 suka jikkata a hare haren kunar bakin wake biyu da aka kai a yankin Hadjer Lamis kusa da tafkin Chadi.

An kai hari na farko ne a garin Guitte, inda wani dan kunar bakin wake akan babur ya tada bam da ya dauke da shi inda ya hallaka mutun guda ya yin da mutane 32 suka jikkata.

Hari na biyu kuma an kai ne a garin Mitterine inda aka hallaka mutane 2 ya yin da mutane 24 suka jikkata.

Wadannan hare hare guda biyu dai an kai su a yankunan da rundunar sojoji ta hadin gwiwa a yankin tafkin Chadi ke sintiri domin tabbatar da tsaro.