Dakarun MDD sun ci zarafin yara a Congo

Sojan Majalisar Dinkin Duniya a bakin aiki Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An dade ana zargin dakarun wanzar da zaman lafiyar da cin zarafin mata.

A karon farko Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana kasashen da dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar suka fito, wadanda suka ci zarafin yara a Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo.

Mutanen da ake zargi sun fito ne daga kasashen Bangladesh, da kasar Congon kan ta, da jamhuriyar Nijar da kuma Senegal.

Kiris ya rage babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya Anthony Banbury ya barke da kuka, a lokacin da ya ke sanar da sakamakon binciken cin zarafin yara da aka gudanar, a wani taron manema labarai da aka yia birnin New York.

A watan da ya wuce wani kwamitin bincike mai zaman kan sa ya yi Allawadai da halin ko in kula da Majalisar Dinkin Duniya ta nuna kan zargin cin rafin yaran.