Idris Deby ya zama shugaban AU

Hakkin mallakar hoto
Image caption Sabon Shugaban Tarayyar Africa AU, Idris Deby (a tsakiya) tare da shugabannin kasashen Nijar da Benin da kuma Najeriya.

An nada shugaba Idris Debby a matsayin sabon shugaban kungiyar Tarayyar Africa, AU.

An nada Mista Deby ne a taron da shugabannin kasashen Africa ke yi a Addis Ababa, babban birnin Ethiopia.

Mista Deby ya canji shugaban Zimbabwe Robert Mugabe bayan da ya kammala wa adinsa.

A waje guda kuma sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya baiyana goyon bayansa da shirin tura sojin kiyaye zaman lafiya na Afirka zuwa Burundi.

Ya baiyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron kolin shugabannin kungiyar tarayyar Afirka a kasar Ethiopia inda shugabannin ke shirin kada kuri'a domin amincewa da tura sojojin.

Shugaban Burundi Pierre Nkurunziza ya yi watsi da shawarar.

Kudirinsa na yin tazarce karo na uku a karagar mulki ya haifar da zanga zangar da aka shafe watanni ana yi a kasar.

Shugaban Gambia Yahya Jammeh wanda ya hau shugabanci bayan juyin mulki ya ce ba zai kada kuri'a domin tura sojoji ba tare da amincewar Burundi ba