Yau za a yi walimar Kanywood Awards

Hakkin mallakar hoto Nasiru B Mohammed
Image caption A shirya dandalin da za a gudanar da walimar Kanywood Award a Kaduna .

A daren yau ne Asabar, za a gudanar da walimar bayyana wadanda su ka ci kyautar Kanywood Awards a Kaduna.

A walimar ce ake sa ran bayyana sunayen wadanda su ka ci kyaututtuka a fanni daban daban a shirin fim.

Wadanda su ka samu nasara kuma aka bayyana sunayen su, su za a mikawa kyaututtuka a bikin da za a yi a ranar 12 ga watan Maris na wannan shekarar.

Image caption Wurin da za a gudanar da walimar Kannywood a Kaduna a inda za a bayyana sunayen wadanda za a ba kyaututtuka a gagarimin bikin da za a gudanar ranar 12 ga watan Maris