Mutane 16 sun mutu a Madaya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kawanayar da aka yiwa Madaya a Syria ya sa mutanen garin a cikin halin yunwa da kunci

Kungiyar agaji ta likitoci ta duniya MSF, ta ce wasu karin mutane goma sha shida ne su ka mutu a Madaya ta Syria wadda aka yi wa kawanya, tun bayan da aka kyale motocin agaji su kai taimako.

Kungiyar ta ce da akwai sama da mutane dari uku wadanda ke fama da larurar rashin cin abinci, yayin da akalla mutane talatin ke cikin halin rai kwakwai, mutu kwakwai.

Rahoton da kungiyar agajin ta fitar ya zo ne a daidai lokacin da ake kokari tattaunawa a Geneva domin kawo karshen yakin Syria wanda aka yi shekara biyar ana yi.