Jirgin ruwa ya kife da yan cirani a Girka

Hakkin mallakar hoto AP

Kafofin yada labaran Turkiya sun ce mutane 39 ciki har da yara kanana sun nutse a ruwa yayin da suke kokarin ketara kogin Aegean zuwa cikin Girka.

An sami ceto wasu mutanen fiye da sittin.

Sojoji masu tsaron gabar ruwa sun ce mutanen suna kokarin zuwa tsibirin Lesbos ne inda dubban yan gudun hijira suka isa a yan makonnin da suka wuce a kan hanyar su ta zuwa arewacin turai.

Mazauna yankin sun ce kuwar da mutanen da ke cikin jirgin suka rika ta tashe su a cikin dare.

An ruwaito cewa an kama mutum daya bisa safarar mutane.

Sai dai wakilin BBC a Turkiya yace wadanda ake kamawa galibin su yan kore ne maimakon manyan masu aikata miyagun laifukan.